Isa ga babban shafi

An kashe wakilan sulhu na gwamnatin Sudan ta Kudu 7

Wata kungiyar agaji ta kasar Norway ta ce an kashe wasu Wakilan gwamnatin sudan kudu 7 da suka halarci zaman tattaunawar neman zaman lafiya a kudu maso gabashin kasar 

Wani dan tawaye cikin shiri a kasar Sudan ta Kudu.22/09/2018
Wani dan tawaye cikin shiri a kasar Sudan ta Kudu.22/09/2018 © SUMY SADURNI/AFP
Talla

Jami’an dai sun gamu da ajalinsu ne a yankin Imehejek dake gabashin jihar Equitoria, a hanyarsu ta dawowa daga wani taron tattaunawar sulhu domin kashe wutan rikici da ya kunno kai tsakanin wasu kabilun manoma da makiyaya.

Cikin sanarwar da shugaban kungiyar Dagfinn Hoybraten ya fitar, yace harin na baya bayan nan ya fito da hatsarin dake tattare da aiki a yankunan da yanayin tsaronsu ka iya canzawa a kowanne lokaci, kana ya ya yi tir da harin da aka kai wa fararen hula da masu aikin agaji. 

Ya zuwa yanzu dai babu wani karin bayani dangane da faruwar lamarin, yayin da kungiyar ta ce ana gudanar da bincike akai. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.