Isa ga babban shafi

An kama masu fafutukar kare hakkin dan adam 4 a Burundi

An tsare wasu masu fafutukar kare hakkin bil adama 4 a kasar Burundi yayin da suke kokarin tafiya Uganda domin ganawa da kungiyoyin fararen hula.

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza yayin wani rangadi a shekarar 2015.
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza yayin wani rangadi a shekarar 2015. AP - Berthier Mugiraneza
Talla

Da yake magana bisa sharadin sakaya suna saboda fargabar daukar mataki a kansa, shaida a filin tashi da saukar jiragen sama na Bujumbura da ma'aikatan tsaro da hukumar kare hakkin bil'adama ta kasa sun shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa jami'an hukumar leken asiri ta kasar ne suka kama mutanen da safiyar Talata.

Kawo yanzu dai ba a san dalilin da ya sa aka kama mutanen ba. Irin wannan kame dai ya zama ruwan dare a 'yan shekarun nan a kasar ta Burundi, inda masu sa ido ke zargin gwamnatocin da ke ci a yanzu da na baya da laifin cin zarafi da kuma dakile 'yan adawa.

Anschaire Nikoyagize, shugaban kungiyar Ligue Iteka, wata kungiyar kare hakkin dan adam mafi tsufa a kasar, ya tabbatar da kamen mutanen hudu.

Wadanda aka tsare su ne Audace Havyarimana, wakilin shari'a na kungiyar zaman lafiya da inganta 'yancin dan adam; Sylvana Inamahoro, babban daraktan kungiyar; Sonia Ndikumasabo, shugabar kungiyar lauyoyi mata ta Burundi; da Marie Emerusabe, babbar jami’ar kungiyar.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga hukumomin Burundi, amma babban mai gabatar da kara Sylvestre Nyandwi da mai magana da yawun ofishin mai gabatar da kara, Agnès Bangiricenge, ba su amsa bukatar yin sharhi ba.

A wata ziyara da ya kai Burundi a baya-bayan nan, wakili na musamman na kungiyar Tarayyar Turai mai kula da sashen kare hakkin bil'adama, Eamon Gilmore, ya bayyana damuwarsa game da yadda ake take hakkin bil'adama a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.