Isa ga babban shafi

An fara shari'ar 'yan tawayen da suka kashe shugaba Idris Deby a Chadi

An fara shari’ar wasu ‘yan tawaye 150 da ake zargi da hannu a kisan shugaban kasar Chadi Idriss Deby a shekarar 2021, shari’ar da aka faro karkashin tsauraran matakan tsaro a gidan yarin Klessoum.

A ranar 23 ga watan Aprilun 2021 ne 'yan tawayen suka kashe shugaban lokacin da ya ke jagorancin dakarun Sojin kasar a wata gwabzawa.
A ranar 23 ga watan Aprilun 2021 ne 'yan tawayen suka kashe shugaban lokacin da ya ke jagorancin dakarun Sojin kasar a wata gwabzawa. REUTERS - POOL
Talla

‘Yan tawayen na kungiyar FACT wadanda suka yi yunkurin hambarar da gwamnatin ta Chadi daga sansaninsu da ke kasar Libya, majiyoyin shari’ar da ke tabbatar da fara sauraron karar sun bayyana cewa za a gudanar da shari’ar tare da yanke hukuncin cikin sirri.

‘Yan tawayen dai na fuskantar zarge-zargen ta’addanci tilastawa yara shiga aikin soja da kuma shiga aikin sojin da kuma kalubalanta tsaron kasa baya kisan shugaba mai ci.

A watan Aprilun 2021 ne ‘yan tawayen suka yi zuga tare da nufar birnin Ndajema a wani yunkuri na kifar da gwamnati lamarin da ya sanya shugaba Deby jagorantar dakarun Sojin kasar tare da tararsu akan hanya, lamarin da ya kai ga rasa ransa.

Da taimakon Faransa ne Chadi ta iya nasarar kora ‘yan tawaye sai dai tattaunawa tsakaninsu da gwamnati ta tsaya cak tun bayan nadin Mahamat Deby shekaru 2 da suka gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.