Isa ga babban shafi

Al-Qaeda ta dauki alhakin hare-haren da suka kashe mutane 5 a Mali

Kungiyar Al-Qaeda ta dauki alhakin hare-hare biyu da suka kashe mutane 5 da suka hada da fararen hula uku da jami’an tsaro 2 ranar Litinin a Mali.

Sojojin kasar Mali
Sojojin kasar Mali © AFP/Souleymane Ag Anara
Talla

Mayakan kungiyar na Al-Qaeda sun kai hare-haren ne a a garuruwan Markacoungo da Kassela da ke kan babbar hanyar Bamako zuwa Ségou a kudu maso gabashin Mali, yankin da ba kasafai ake fuskantar matsalar ta’addanci ba.

Kasar Mali da ke yankin Sahel ta kwashe shekaru goma tana fafatawa da 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi, wanda daga bisani ya bazu zuwa makwafciyarta Nijar da Burkina Faso.

Gwamnatin mulkin sojan kasar da ke kan karagar mulki tun daga shekarar 2020 ta kawo sojojin haya daga Rasha na kamfanin Wagner, wadanda take gabatar da su a matsayin malaman soja don taimaka mata yaki da ‘yan ta’addda.

Matakin dai ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin Malin da kasashen Yammacin Turai, musamman Faransa da a shekarun baya ta yi mata mulkin mallaka, sakamakon daukar sojojin hayar na kamfanin Wagner mamsu kutse da suke tamkar wakilan gwamnatin shugaba Vladimir Putin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.