Isa ga babban shafi
Mali-Sahel

Gwamnatin Mali za ta tattauna da 'yan ta'adda

Gwamnatin Mali ta ce a shirya take ta shiga tattaunawa da kungiyoyin da ke dauke da makamai musamman a yankin tsakiya kasar, kamar dai yadda kungiyar International Crisis Group ICG ta bayar da shawara.

Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keita, na jagorantar taron sulhunta 'yan kasar
Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keita, na jagorantar taron sulhunta 'yan kasar AFP Photo/Michele CATTANI
Talla

Ministan tsaron cikin gidan kasar Mali Boubacar Alpha Ba, ya ce gwamnatin na cikin shiga wannan tattaunawa, kuma tuni ta fara aiki dangane da wannan batu.

Bayan share tsawon lokaci tana bincike a game da ayyukan kungiyar ‘yan ta’adda da ake kira Macina Katba da ke karkashin jagorancin Amadou Koufa, kungiyar ta ce ta hnyar shiga tattaunawa ne kawai za a iya shawo kan kungiyar domin ta daina kai hare-hare a yankin tsakiyar kasar ta Mali.

To sai dai manazarta na ganin cewa tattaunawar za ta iya kasancewa mai wuya, lura da yadda tuni shugaban kungiyar Amadou Koufa ya yi mubaya’a ga wasu kungiyoyin ta’addanci da suka hada da Alqa’ida da kuma Aqmi, lamarin da zai sai da wuya malamin ya iya daukar mataki ba tare da amincewar wadannan kungiyoyi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.