Isa ga babban shafi

An kashe 'yan tawaye 40 a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

An kashe 'yan tawayen Burundi 40 a wani farmakin hadin gwiwa da sojojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Burundi suka kai a gabashin Congo.

Kasar dai ta dade tana fama da tashe-tashen hankula na masu dauke da makamai
Kasar dai ta dade tana fama da tashe-tashen hankula na masu dauke da makamai AFP/Archivos
Talla

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Laftanar Marc Elongo-Kyondwa ya ce sojojin biyu "sun kai wani gagarumin farmaki" kan 'yan tawayen Burundi.

Ya kara da cewa sojojin biyu sun fatattaki ‘yan tawayen FNL daga dukkan tsaunuka hudu da ke yankin Nabombi.

Sanarwar ta ruwaito Janar Ramazani Fundi, kwamandan ayyuka a yankin kudancin kasar Congo yana cewa, rundunar sojojin Congon ta yi kira ga al'ummar yankin da su ba da hadin kai ga sojojin, sannan kuma matasa su ware kansu daga kungiyoyin da ke dauke da makamai".

Tun a watan Agusta, sojojin Burundin ke yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai a yankin Kivu ta Kudu, a matsayin wani bangare na rundunar kungiyar kasashen gabashin Afirka (EAC).

A cikin watan Yuni, EAC ta yanke shawarar kafa rundunar yankin da ta kunshi sojojin Kenya da Uganda tare da sojojin Congo a arewacin Kivu da Ituri, da sojojin Sudan ta Kudu da ke Haut-Uele da kuma Burundi a kudancin Kivu.

Kinshasa da ke zargin Rwanda da goyon bayan 'yan tawayen M23 a arewacin Kivu, ta ki yarda Kigali ta shiga cikin rundunar.

Kimanin shekaru 30 kenan gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ke fama da kungiyoyin masu dauke da makamai, wasu na cikin gida, wasu kuma daga kasashe makwabta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.