Isa ga babban shafi

Karancin ruwa da abinci ya kashe giwaye 200 da tarin namun daji a Kenya

Giwaye fiye da 200 da kuma daruruwan jakunan dawa da kuma ragunan na dawa ne suka mutu, sakamakon fari mafi tsanani cikin shekaru 40 da ake gani a Kenya.

Wasu giwaye a Kenya.
Wasu giwaye a Kenya. AP - Charmaine Noronha
Talla

Yayin da yake karin bayani kan halin da ake ciki a wani taron manema labarai a birnin Nairobi, ministan yawon bude ido Peninah Malonza, ya ce yanzu haka Ibtila’in farin mai tsanani ya shafi kusan rabin yankunan Kenya da kuma akalla mutane miliyan hudu daga cikin miliyan 50 na kasar.

Ministan ya kara da cewa akasarin namun dajin da farin ya halaka masu rayuwa kan abinci nau'in ciyawa.

Kididdigar da gwamnatin Kenya ta wallafa a baya bayan nan, ta nuna cewar, tsakanin Fabrairu da Oktoban shekarar 2022 da muke, giwaye 205, da ragunan dawa 512, da Jakunan dawa 381, da rakuma 12 da kuma bauna 51 suka mutu sakamakon tsananin farin da ya addabi sassan kasar.

A shekarar bara ma’aikatar harkokin yawon bude idon Kenya ta ce akwai giwaye 36,000 a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.