Isa ga babban shafi

Giwaye na cigaba da kai hari tareda kisan jama'a a Zimbabwe

Akalla mutane 60 giwaye suka kashe a wannan shekarar ta 2022 a kasar Zimbabwe,wanda kuma duk da nasarorin da masu tsaron gandun daji ke samu ana kara samun rashin jituwa tsakanin su da mutanen yankunan.

Giwaye a kasar Bostwana
Giwaye a kasar Bostwana AFP/File
Talla

Sabanin yadda yake a sauran kasashen duniya inda ake asaran giwayen saboda mutane na kashe su don samun hauren su,a Zimbabwe yawan giwayen karuwa yake da kashi biyar cikin dari kowace shekara.

A wasu yankunan giwayen suna kiwo ne kuma a hakan har cimma gidajen mutane,wanda hakan ke sa mutane su far musu har aji musu rauni, kamar yadda mai magana da yawun gwamnati Nick Mangwana ya sheidawa manema labarai.

Wasu daga cikin giwaye a gidan kalo na kasar Zimbabwe
Wasu daga cikin giwaye a gidan kalo na kasar Zimbabwe AFP

Rikici tsakanin giwaye da mutane ya zama wata babbar matsala da kullum karuwa take inda a wannan shekarar kadai mutane 60 sukayi asaran rayukan su yayin da 50 kuma suka samu rauni.

Kasar Zimbabwe na da giwaye sama da 100,000 wanda inda itace kasa ta biyu a duniya mafi yawan giwaye bayan Botswana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.