Isa ga babban shafi

Yawan al'ummar Tanzania ya karu da kusan kashi 40 cikin shekaru 10

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta ce sakamakon kidayar jama'ar da kasar ta gudanar ya nuna yadda aka samun karuwar yawan al’umma da fin kashi 37 wanda ke nuna yadda adadin 'yan kasar zuwa yanzu ya kai miliyan 61 da dubu dari 7.

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan.
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan. © NewTimesRwanda
Talla

Alkaluman kidayar jama'ar ta Tanzania ya nuna karuwar jama'a mafi yawa irinsa na farko da kasar ta ganin, lamarin da shugaba Suluhu ke kashedi a kan kalubalen da ke tattare da karuwar yawan al’umma.

Da ta ke bayyana sakamakon kidayar jama’ar kasar a jiya Litinin, shugaba Suluhu Hassan ta ce cikin shekaru 10 da suka gabata yawan jama'ar Tanzania ya karu da kusan kashi 40, wanda ke nuna gagarumin aikin da ke gaban hukumomi da kuma daidaikun mutane don tunkarar kalubalen da ke tafe da karuwar jama'a.

Yawan al’ummar kasar da ke gabashin Afrika ya karu daga miliyan 44 da dubu dari 9 daga shekarar 2012 zuwa miliyan 60, kamar yadda sakamakon kidayar jama’a da aka yi a farkon wannan shekarar ya nuna.

Shugaba Hassan ta ce alkaluma sun nuna cewa ana samun karuwar jama’a da sama da kashi 3 a kasar duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.