Tanzania: Sama da kashi 90 na daliban nazarin aikin lauya ne suka fadi jarabawa
Lauyoyi a kasar Tanzaniya sun nuna damuwa bayan rahotannin da ke cewa dalibai 26 ne kawai daga cikin 633 ne suka samu nasarar cin jarabawa a kwalejin nazarin aikin lauya, wanda ke nuna adadin da kashi 4.1 cikin dari.
Wallafawa ranar:
Jaridar Mwananchi ta ruwaito cewa dalibai 342 ne aka yi hasashen za su samu nasara a jarrabawar, yayin da wasu 265 aka dakatar da su baki daya.
Wadanda suka kammala karatu daga jami’o’i daban-daban sai sun ci jarrabawar a kwalejin nazarin aikin lauya kafin a rantsar da su a matsayin lauyoyi.
An dora alhakin rashin nasarar daliban da aka samu dai a kan rashin inganta harkokin jami'o'in kasar, kamar yadda mahukuntan kwalejojin shari'a suka ruwaito.
Ko a shekarun da dama da suka gabata ma an samu raguwar nasarar dalibai, amma sakamakon bana ya kasance mafi muni a cikin ‘yan shekarun nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu