Isa ga babban shafi
Tanzania

Tanzania ta yi karin mafi karancin albashi ga ma'aikata

A jiya Asabar shugabar Tanzania ta amince da karin  kusan kaso 25 na albashi mafi karanci ga ma’aikatan kasar, lamarin da ke nuni da hannun riga da manufofin shugaban da ta gada, marigayi John Magafuli.

Shugabar  Tanzania Samia Suluhu Hassan.
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan. © blog.ikulu.go.tz
Talla

Shugaba  Samia Suluhu ta yanke shawarar yin kari na kaso 23 a kan albashin ma’aikatan gwamnatin kasar ne a karon farko tun bayan shekafrar 2016, kamar yadda ofishinta ya bayana a wata sanarwa.

Sanarwar ta ce an yi wannan karin ne duba da yadda tattlin arzikin kasar ya tabarbare sakamakon abubuwan da ke faruwa a ciki da wajen kasar.

Tun da ta dare karagar mulki a shekarar da ta gabata biyo bayan mutuwar shugaba John Magafuli, Hassan ta yi kokarin kauce wa wasu daga cikin manufofinsa, inda ta tattauna da abokan hamayya, tare da soke wasu daga matakan ko in kula da ya dauka a kan annobar Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.