Isa ga babban shafi
Tanzania - IMF

Asusun IMF zai tallafawa Tanzania da dala miliyan 567

Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, ya amince da baiwa Tanzania dala miliyan 567 a matsayin taimakon gaggawa don taimaka wa kasar wajen samun nasarar yiwa al’ummar ta allurar rigakafin Korona, gami da karfafa tsarin kiwon lafiya, da kuma farfado da tattalin arzikin kasar da annobar ta kassara.

Wasu ma'aikatan lafiya da ke yaki da yaduwar cutar Korona a Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzania. 27 ga watan Mayu, 2020.
Wasu ma'aikatan lafiya da ke yaki da yaduwar cutar Korona a Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzania. 27 ga watan Mayu, 2020. REUTERS - Stringer .
Talla

Idan za a iya tunawa dai barkewar cutar Korona da ta tilasata wa kasashe daukar matakin sanya takunkuman hana tafiye-tafiye,  ya haifar da durkushewar harkar yawon bude ido a kasar ta Tanzania da ke Gabashin Afirka, wadda a waccan lokacin ta rika musanta wanzuwar annobar a karkashin marigayi shugaba John Magufuli.

Tsohon shugaban ya karfafa matsayin sa ne kuma bayan da sakamakon da kwararrunsa suka gabatar na cewa sun gano cewar, Akuya, Man Fetur, har ma da Gwanda duk sun kamu da cutar ta Korona, abinda ya sanya Magafuli bayyana wanzuwar annobar a matsayin almara.

Sai dai bayan rasuwarsa, a shugabanci ya koma hannun Samia Suluhu Hassan, gwamnatin kasar Tanzania ta amince da cutar a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.