Isa ga babban shafi
Tanzania-Coronavirus

Shugaban Tanzania yayi amai ya lashe kan tasirin annobar Korona

A wani mataki na bazata, shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya sauya matsayin sa na kin yadda da wanzuwar annobar Korona a kasar, inda a karshen makon nan, ya bayyana cewar al’ummar kasar na da ‘yancin amfani da takunkuman rufe baki da hanci, domin samun kariya daga cutar dake cigaba da aika mutane barzahu a sassan duniya.

Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli
Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli AP
Talla

Shugaba Maghafuli dai yayi kaurin suna wajen yin watsi da tasirin annobar Korona da ya rika bayyana shakku kanta, abinda yasa a watan Afrilu yah ana fitar da alklumman masu kamuwa da cutar da kuma wadanda ta halaka.

A waccan lokacin shugaban na Tanzania ya bukaci ‘yan kasar da su yaki annobar ta hanyar addu’a da kuma rungumar magungunan gargajiya.

Yanzu haka dai gwamnatin Tanzania na shan caccaka bayan bayyanar wani hoton bidiyon ministan kudin kasar Philip Mpango yana tari gami da fama da sarkewar numfashi, a yayin da yake, kokarin karin bayan kan halin da lafiyarsa ke ciki.

Duk da matsalar da yake fama da ita, ministan yaki bayyana cutar dake damunsa, wadda wa su ke fargabar mai yiwuwa Korona ce.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.