Amurka ta zargi Tanzania da boye adadin masu cutar corona
Shugaban John Magafuli na Tanzania yace a wata mai kamawa, wato 1 ga Yuni, za a bude ilahirin manya da kananan makarantun kasar, zalika za a koma wasanni, bayan fuskantar dokar killace jama’a.
Wallafawa ranar:
Magafuli yace addu’o’i ne suka ceto kasar daga tsanantar annobar ta coronavirus.
Masu caccakar matakin shugaba Magafuli na ganin gwamnatinsa na boye adadin masu dauke da cutar ga duniya ne, inda a nasa bangaren ofishin jakadancin Amurka a kasar yace akwai mutane masu yawa da annobar ke kashewa amma gwamnatin ta Tanzana ta gaza daukar matakin basu kariya.
Makwanni 3 kenan dai rabon da Tanzania da sanar da adadin masu dauke da cutar ta coronavirus, bayan mutuwar mutane 16, daga cikin mutum 480 da gwamnati ta sanar sun kamu da ita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu