Isa ga babban shafi
Tanzania

Mutane 20 sun halaka a turmutsutsin shafar tsarkakakken mai

Jami’an lafiya a Tanzania sun tabbatar da mutuwar mutane 20, sakamakon tattake su da aka yi yayin turmutsutsin da aka samu a wurin wani taron Mujami’ar Evengelical da ya gudana a garin Moshi dake arewacin kasar.

Yadda filin taron Mujami'ar Evengilical ya hautsine, bayan wa'azin da Fasto Boniface Mwamosa ya jagoranta a garin Moshi dake arewacin Tanzania.
Yadda filin taron Mujami'ar Evengilical ya hautsine, bayan wa'azin da Fasto Boniface Mwamosa ya jagoranta a garin Moshi dake arewacin Tanzania. REUTERS/Emmanuel Herman
Talla

Kwamishinan lura da yankin Kippi Warioba ya ce an samu turmutsutsin ne bayan da wani fitaccen fasto Boniface Mwamosa ya zubar da wani mai a kasa, da yace mai tsarki, hakan tasa jama’a soma yin kundunbala domin samun tubarraki, da kuma samun waraka daga cutuka.

Akwai dai fargabar karuwar adadin wadanda suka mutu, la’akari da cewa akalla mutane 16 ne suka jikkata sosai.

Wasu ganau, sun ce ganin yadda filin taron ya yamutse abinda ya kai ga rasa rayuka, Fitaccen mai wa’azin wato Mwamposa ya tsere, sai dai bayan baza shelar farautarsa, ‘yan sanda sun yi nasarar kame shi da kuma wasu karin mutane 7 a babban birnin kasarta Tanzania Dar es Salaam.

Tuni dai shugaban kasar John Magufuli ya aike da sakon alhinin mutuwar mutanen 20 a dallin turmutsutsin da kuma wasu 20 da suka mutu a dalilin ambaliyar ruwan da ta akfawa lardin Lindi dake kudancin kasar a makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.