Isa ga babban shafi
Tanzania

Akuya da Gwanda sun kamu da coronavirus a Tanzania - Magafuli

Shugaban Tanzania John Magafuli yayi zargin cewar jami’an kula da lafiyar kasar na coge wajen bada alkaluman mutanen da suka kamu da cutar coronavirus, inda ya bukaci gudanar da bincike kan lamarin.

Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli a babban birnin kasar Dar es Salaam.
Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli a babban birnin kasar Dar es Salaam. REUTERS/Sadi Said
Talla

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar, Magafuli ya bayyana shakku game da binciken da ake kan cutar, inda yake cewa wasu daga cikin wadanda aka gwada cewar suna dauke da cutar ko ciwon kai basa yi.

Shugaban yace a boye, ya sa an gudanar da gwaji kan akuya da gwanda da man mota a dakin gwajin kuma duk sun nuna cewar suna dauke da cutar.

Magafuli yace ko dai na’urorin gwajin basa aiki, kuma ma’aikatan na coge game da gwajin.

Ya zuwa yanzu an gano mutane 480 da suke dauke da cutar a Tanzania, yayin da 16 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.