Isa ga babban shafi
Tanzania

Yan sandan Tanzania sun kame 'yan adawa da dama

'Yan sandan Tanzania sun kame wasu ‘yan babbar jam'iyyar adawa ta Chadema da dama a jiya Asabar, a wani matakin ci gaba da kokarin murkushe ‘yan adawar da ke neman yin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar.

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Chadema a Tanzania Freeman Mbowe da ke fuskantar tuhumar tallafawa ta'addanci.
Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Chadema a Tanzania Freeman Mbowe da ke fuskantar tuhumar tallafawa ta'addanci. Ericky BONIPHACE AFP/File
Talla

Tuni dai ake tsare da shugaban jam’iyyar adawar ta Chadema Freeman Mbowe bisa zargin ta’addanci, wanda magoya bayansa suka bayyana a matsayin tuggun siyasar gwamnatin Shugaba Samia Suluhu Hassan domin dakile su.

Mbowe na tsare a gidan yari tun ranar 21 ga watan Yuli lokacin da aka cafke shi tare da wasu manyan jami'an Chadema sa'o'i kafin su gudanar da taron kiran sabon kundin tsarin mulki, bisa tuhumarsa ne kuma da laifin tallafa wa ta'addanci da hada baki domin cutar da kasa.

A ranar Litinin jagoran ‘yan adawar zai sake bayyana a babbar kotun Tanzania don ci gaba da fuskantar sharia’

A baya bayan nan 'Yan sanda suka tsare' yan babbar jam'iyyar adawar ta Chadema 9 t tare da kai samame ofisoshinsu a garin Musoma don hana taron matasa da aka shirya kan canjin neman sauya tsarin mulkin Tanzania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.