Isa ga babban shafi
Tanzania-Siyasa

Hukuncin kotu ya haddasa rikici a Tanzania

Mummunan rikici ya barke a Tanzania bayan da wata kotu ta kama babban jagoran adawar kasar da laifin ta’addanci.

Jagoran 'yan adawar Tanzania Freeman Mbowe tare da magoya bayansa
Jagoran 'yan adawar Tanzania Freeman Mbowe tare da magoya bayansa Ericky Boniphace AFP/Archivos
Talla

Tuni dai babbar jam’iyyar adawa ta kasar za zargi gwamnati da kulla kutungwilar da ta sanya aka lankaya wa jagoran nasu wannan laifi na ta’adanci.

An dai zargi jagoran ‘yan adawa Freeman Mbowe da laifin ta’addancin ne a wata kotun da ke babban birinin kasar, Dar Es Salam.

Jam’iyyar adawa ta kasar ta zargi kotun da yanke hukunci bisa zalunci, la’akari da yadda aka hana ‘yan uwansa da kuma lauyoyinsa shiga harabar kotun.

Bayan laifin ta’adancin, ana kuma zargin Mbowe da laifin taimaka wa ‘yan ta’adda da goya musu baya da kuma cin dunduniyar tattalin arzikin kasar, wanda kuma babu damar bada belin wanda ake zargi da wadannan laifuka bisa kundin tsarin mulkin kasar.

Tun a makon jiya ne, jami’an tsaro suka cafke Mbowe mai shekaru 59 tare da wasu mambobin jam’iyyar adawar kasar, kwanaki kadan kafin gudanar da babban taron jam’iyyarsu ta Chadema na kasa da suka shirya don yi wa kundin tsarin jam’iyyar kwaskwarima.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.