Isa ga babban shafi
Tanzania

Yan kasar Tanzania sun yi ban kwana da Magufuli

Sabuwar shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta jagoranci mutanen kasar wajen yiwa gawar tsohon shugaban kasa John Magufuli ban kwana yau a birnin Dar es Salam.

Jana'izzar marigayi John Magufuli na kasar Tanzania
Jana'izzar marigayi John Magufuli na kasar Tanzania REUTERS - STRINGER
Talla

Rahotanni sun ce tarin jama’ar kasar sun yi jerin gwano wajen yiwa gawar ban kwana, yayin da wasu ke zub da hawaye, wasu kuma na jefa firanni a kan akwatin gawar wadda sojoji suka dauka daga mujami’a zuwa filin wasan Uhuru domin karrama ta.

Sabuwar Shugabar tanzania  Samia Suluhu Hassan
Sabuwar Shugabar tanzania Samia Suluhu Hassan REUTERS - STRINGER

Suluhu Hassan da aka rantsar jiya a matsayin mace ta farko da ta zama shugabar kasar ta jagoranci manyan jami’an gwamnati wajen tattaki domin wuce akwatin gawar Magufuli da aka lullube da tutar Tanzania suna yi mata ban kwana da kuma mika sakon ta’aziya ga uwargidan sa.

Mutane da dama sun sanya bakaken kaya ko kuma masu dauke da launin tutar Jam’iyyar dake mulkin kasar, amma kadan daga cikin su ne suka sanya kyallen dake rufe baki da hanci a kasar da ake tababar cutar korona.

Gwamnatin Tanzania ta bayyana zaman makoki na makwanni 3 bayan sanar da rasuwar shugaba Magufuli a wani asibitin dake Dar es Salam.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.