Isa ga babban shafi
Tanzania - Magufuli

Al'ummar Tanzania na ci gaba da makokin shugaba John Magufuli

Ana cigaba da zaman makoki a kasar Tanzania sakamakon rasuwar shugaban kasa John Magufuli, yayin da ake saran rantsar da mataimakiyar sa Samia Saluhu Hassan a matsayin wadda zata gaje shi domin kamala wa’adin mulkin sa. Yan kasar na cigaba da bayyana ra’ayoyi daban daban dangane da rashin da aka yi.

Tsohon shugaban kasar Tanzania, John Magufuli.
Tsohon shugaban kasar Tanzania, John Magufuli. Tanzania State House Press/Handout via REUTERS
Talla

Yayin da ake zaman makokin, babban dan adawar kasar, Tundu Lisu ya zargi gwamnati da yin karya, inda ya ce tun a makon jiya shugaba Magufuli ya mutu.

''Cutar korona ce ta kashe Magufuli, abu na farko kenan, na biyu, Magufuli bai mutu yau da yamma ba, ina da labari daga majiyar da ta fada min cewar yana fama da tsananin rashin lafiya, ina da labarin ke cewar Magufuli ya mutu tun ranar larabar makon jiya. Abinda kawai ya bani mamaki shi ne yadda suka ci gaba da yin karya, har zuwa yanzu da ya mutu Gwamnatin sa na cigada da yin karya''.

Shi kuwa kakakin Jam’iyya mai mulki Humprey Polepole ya bukaci kwantar da hankali ne kamar haka

''Shugabannin Jam’iyya sun bukaci magoya bayan su da masu mana fatar alheri da su kwantar da hankalin su da cigaba da jajircewa yayin da suke nazarin kan irin gagarumar gudumawar da shugabanmu John Pombe Joseph Magufuli ya bayar''.

A nasa bangare kakakin 'yan adawa Salim Biman kira ya yi wajen ganin an aiwatar da abinda kundin tsarin mulki ya fadi.

''Muna saran a mutunta kundin tsarin mulkin kasar mu da kuma aiwatar da shi a wannan mawuyacin lokaci domin baiwa kasar mu hadin kai da fahimtar juna''.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.