Isa ga babban shafi
Tanzania

Babbar jam'iyyar adawar Tanzania ta ce ba za ta amince da sakamakon Zabe ba

Babban Jam’iyyar adawar Tanzania ta ce ba za ta amince da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi jiya ba, saboda zargin tafka magudin da ta ce anyi wanda ya bai wa Jam’iyya mai mulki damar lashe kujerun majalisu mafi muhimmanci a kasar.

Wasu daga cikin masu zabe a ruhunan zabe a kasar Tanzania
Wasu daga cikin masu zabe a ruhunan zabe a kasar Tanzania RFI
Talla

Hukumar zaben Tanzania ta ce sakamakon farko daga mazabu 12 daga cikin 264 sun nuna cewar shugaba John Magufuli da ke neman wa’adi na biyu na kan gaba da kashi 80 wajen ganin Jam’iyyar sa ta Chama Cha Mapinduzi ta ci gaba da rike mulki tun daga shekarar 1961.

Sakamakon ya nuna cewar babban dan adawa Tundu Lissu na bi masa da kashi 15, kuma tuni ya bayyana sakamakon a matsayin haramtacce ya kuma bukaci magoya bayan sa da su gudanar da zanga zangar lumana, yayin da ya yi kira ga kasashen duniya da kar su amince da sakamakon.

Lissua ya ce abinda ya faru jiya ba zabe bane, saboda haka ba su amince da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.