Isa ga babban shafi
Tanzania

Al'ummar Tanzania na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

Yau Laraba al’ummar Tanzania da na yankin Zanzibar ke kada kuri’a a babban zaben kasar wanda ‘yan takara 15 ke shirin fafatawa inda shugaba John Magafuli ke neman wa’adin mulki na biyu na tsawon shekaru 5 a nan gaba.

Wasu masu kada kuri'a a Tanzania.
Wasu masu kada kuri'a a Tanzania. Reuters
Talla

Tun da misalin karfe 7 na safiyar yau aka bude rumfuna zabe a sassan kasar ta Tanzania da kuma yankin na Zanzibar mai kwarya-kwaryan ‘yanci.

Fiye da mutane miliyan 29 ake saran su kada kuri’a a zaben na yau cikin kasar wadda jam’iyyar TANU ke jagoranci tun bayan ‘yancin kai a shekarar 1961.

Babban zaben Tanzaniar da tsibirin Zanzibar wanda ya kunshi na shugaban kasa da ‘yan Majalisun dokoki, shugaba Magafuli mai shekaru 61 na neman wa’adi na biyu ne inda Tunda Lissu mai shekaru 55 ke matsayin babban abokin dabinsa wanda kuma ke da tarin magoya baya.

Sauran ‘yan takarar sun hada da Bernard Membe mai shekaru 66 kana Seif Sharif Hamad mai shekaru 77 tukuna Hussein Mwinyi mai shekaru 53.

Gabanin zaben na gobe dai, an samu rikici baya ga jita-jitar kisa a wasu sassa na kasar.

A bangare guda al’ummar Tanzania sun jima suna bore da matakin John Magafuli na sake tsayawa takara don neman wa’adin na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.