Isa ga babban shafi
Tanzania

Wasu mahara sun raunata jagoran babbar jam'iyyar adawa a Tanzania

Shugaban babbar jami’iyyar adawa a Tanzania, Freeman Mbowe yana kwance a asbiti bayan afk mai da wasu mhar da ba a san ko su wanene ba suka yi.

Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli.
Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli. REUTERS/Thomas Mukoya/File Photo
Talla

Wata sanarwa daga ofishin ‘yan sandn yankin ta ce labari ya ishe ta cewa wasu mutane uku ne suka afka wa Mbowe har sai da suka karya mai kafarsa ta dama, lamarin d ya sa yake kwance a asbirti halin yanzu.

Jam’iyyarsa ta Chadema ta wallafa a shafinta na Twitter cewa Mbowe yana kan hanyarsa ta komawa gida ne ya gamu da wadannan bata gari da suka yi mai wannan ta’adi.

Mbowe ya sha zargin gwamnatin kasar da rashin shaida wa al’ummar kasar gaskiyar lamari a game da cutar coronavirus a kasar, biyo bayan daina sabanta bayanai a game da cutar da hukumomi suka yi tun a watan Afrilu.

Mbowe da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar daga bangaren ‘yan adawa sun yi zama na dan lokaci a gidan yari sakamakon haramtacciyar zanga zangar adawa da shugaban kasar mai ci John Magufuli wanda ake zargi da murkushe ‘yan adawa da cin zarafin masu suka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.