Isa ga babban shafi

Kungiyoyi da jam'iyyun siyasa sun janye daga tattaunawar makomar Chadi

Gomman kungiyoyi da kuma jam’iyyun siyasa ne suka bayyana janyewarsu daga taron tattaunawa kan makomar Chadi da ke gudana yanzu haka a birnin Ndjamena, inda su ke nuna rashin amincewa da hanyoyin da aka bi wajen zaben wadanda za su jagoranci zaman taron.

Zaman taron tattaunawa kan makomar Chadi bisa jagorancin shugaba Mahamat Idris Deby.
Zaman taron tattaunawa kan makomar Chadi bisa jagorancin shugaba Mahamat Idris Deby. AFP - AURELIE BAZZARA-KIBANGULA
Talla

Shuwagabanin kungiyoyi da dama ne dai da suka hada da na siyasa da farar hula suka bayyan barazanar janyewa daga tattaunawar neman hadin kai da dinke barakar siyasar da kasar ta Chadi ke fama da ita tsawon shekaru.

Daga cikin wadanda suka nuna rashin amincewar ta su da zaben sun hada ne da tsohon dan majalisar dokoki haka kuma tsohon shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar Tchadi Ngarlejy Yorongar et de l’ancien président de la ligue tchadienne des droits de l’homme, Enoch Djondang, rapporte notre correspondant à Ndjamena,Madjiasra Nako « Le gouvernement sera responsable devant dieu et devant la nation de ce qui arrivera », prévient aussi l’entente des églises protestantes. Les Églises et missions évangéliques menacent de suivre le mouvement.

L’ancien ministre Siddick Abdelkerim Haggar, dake shugabanta hadakar jam’iyun siyasa da kungiyoyin farar hula, ya bayyana bin sahun masu neman sauyi da gungun gwagwarmayar Wakit Tamma, kungiyoyi biyun da tun da farko suka bayyana kin amincewa da halartar taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.