Isa ga babban shafi

Kyanda ta kashe kananan yara 157 cikin mako guda a Zimbabwe

Akalla kananan yara 157 cutar kyanda ta kashe a Zimbabwe cikin mako da bullar annobarta a kasar koda ya ke ma’aikatar lafiya ta ce alkaluman ka iya ninkawa saboda rashin tattara cikakkun bayanai.

Cutar kyanda na ci gaba da kasancewa babbar barazanar lafiya ta yadda ta ke lakume rayukan dubban kananan yara a duk lokacin da aka samu bullarta.
Cutar kyanda na ci gaba da kasancewa babbar barazanar lafiya ta yadda ta ke lakume rayukan dubban kananan yara a duk lokacin da aka samu bullarta. REUTERS - HEREWARD HOLLAND
Talla

Bayan bullar cutar a makon jiya, gwamnatin kasar ta zargi majami’ar Apostolic da taimakawa wajen fantsamar cutar saboda yadda ta gaza wajen karfafa gwiwar mutane su karbi rigakafi.

Wasu alkaluma da gwamnatin Zimbabwe ta fitar ta ce galibin wadanda suka harbu da cutar ta kyanda basu karbi rigakafin da aka bayar a baya-bayan nan ba.

Alkaluman na gwamnati sun nuna cewa adadin wadanda suak harbu da cutar a talatar da ta gabata, ya koma yara dubu 2 da 56 sabanin dubu 1 da 36 da aka samu kwanaki 4 bayan bullar cutar.

Ministan yada labarai na Zimbabwe Monica Mutsvangwa a jawabinsa yayin taron masu ruwa da tsaki ya ce galibin wadanda kef ama da cutar suna a tsakanin watanni 6 da haihuwa ne zuwa shekaru 15.

Tuni dai gwamnati ta umarci sashen lafiyar kasar ya karfafa shirinsa na rigakafi yayinda sashen kare lafiyar jama’a kuma zai karfafa aikin wayar da kai don nunawa al’umma muhimmancin karbar rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.