Isa ga babban shafi

Mutane 33 sun mutu a wani mummunan hadarin Mota a Kenya

Akalla Fasinja 33 suka mutu a Kenya yau litinin, bayan motar da su ke ciki ta kufcewa direba tare da fadawa cikin wani kogi wanda ya yi sanadin mutuwar ilahirin mutanen da ke cikin motar.

Motar da aka yi hadarin da ita.
Motar da aka yi hadarin da ita. © Daily Nation
Talla

Rahotanni sun ce a daren jiya lahadi ne hadarin ya faru lokacin da motar ke balaguro daga kauyen Meru zuwa birnin Mombasa da ke gabar teku a kasar ta Kenya.

A cewar jami’an agaji, motar ta nutse nisan mita 40 ko kuma kafa 130 a cikin kogin Nithi bayan da ta kufcewa direban tare da sauka daga kan gadar da ta ratsa kogin.

Wasu hotunan hadarin da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuno yadda motar ta tsage gida biyu yayinda sassanta suka biyo saman ruwa haka zalika gawarwaki.

Jami’an da suka isa wajen bayan faruwar ibtila’in sun ce mutane 20 sun mutu nan ta ke tun a daren jiya lahadi yayinda wasu 4 suka mutu a asibiti yayinda sauran aka gano gawarwakinsu a yau litinin.

Kwamishinan yankin Norbert Komora ya shaidawa manema labarai cewa ana ci gaba da laluben wadanda suka nutse a ruwan.

A baya-bayan nan Kenya na ganin karuwar mutanen da ke mutuwa sanadiyyar hadarin titi inda daga watan Janairu zuwa yanzu ake da alkaluman mutun dubu 1 da 912 fiye da mutum dubu 1 da 754 da aka gani bara a irin wanann lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.