Isa ga babban shafi

Ruto ya yi alkawarin korar ‘yan China da zarar ya zama shugaban Kenya

Mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar neman kujerar shugabancin Kenya, William Ruto, ya yi alkawarin korar ‘yan China da ya bayyana da cewa, sun mamaye ayyukan ‘yan kasar da zarar an zabeshi kan karagar a zaben da za a gudanar a watan Agusta mai zuwa.

Mataimakin shugaban Kenya, kuma dan takarar kujerar shugabancin kasar William Ruto.
Mataimakin shugaban Kenya, kuma dan takarar kujerar shugabancin kasar William Ruto. REUTERS - BAZ RATNER
Talla

Zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da kuma kananan hukumomin da za a gudanar a ranar 9 ga watan Agustan wannan shekara dai na zuwa ne a lokacin da kasar mafi karfin tattalin arziki dake yankin gabashin nahiyar Afrika ke fuskantar matsalar tattalin arziki, sakamakon tasirin annobar Covid-19 da kuma yakin kasar  Ukraine.

Sai dai kuma mataimakin shugaban kasar dake zaman doya da manja a tsakaninsu William Ruto ya ce da zarar ya lashe zaben kasar zai tarkata ‘yan kasar china dake gudanar da kanan sana’o’i a kasar irinsu gasa masara ko kuma tallan wayar salula ya koresu.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar talata ya bayyana gabadaya wadannan ayyuka da zama na ‘yan kasar Kenya amma Sinawa suka kwace su.

Sai dai kawo yanzu Ofishin jakadancin kasar China dake Nairobi bai ce uffan ba dangane da tambayar da kamfanin dillancin labaran AFP ya gabatar masa kan batun.

William Ruto mai shekaru 55 a duniya na bukatar  maye gurbin  shugaban kasar Uhuru Kenyata da baya bukatar sake tsayawa a wani sabon wa’adin mulki karo na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.