Isa ga babban shafi

Odinga da Ruto sun nada abokan takara a zaben Kenya

Manyan ‘yan takarar zaben shugaban kasa a Kenya sun zabi abokan tsayawa takararsu, inda Raila Odinga ya zabi wata fitacciyar mai gwagwarmayar kare hakkin mata, yayin da abokin adawarsa, William Ruto ya zabi wani kwararren masanin yakin neman zabe.

Raila Odinga
Raila Odinga REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Abokan takarar da suka zaba, dukkaninsu sun fito ne daga kabilar Kikuyus wadda ta fi shahara a kasar ta Kenya, yayin da Odinga da Ruto ke kokarin ganin sun samun dimbin kuri’u daga al’ummar wannan kabilar.

Odinga mai shekaru 77, ya zabi Martha Karua , tsohuwar Ministar Shari’ar Kenya wadda ake yi wa lakabi da Iron Lady domin taya shi tsayawa takara a zaben mai tafe.

Tuni dai Karua da a can baya ta taba neman kujerar shugabancin kasar ta bayyana cewa, lokaci ya yi da ya kamata a bai wa mata dama.

Tsohuwar Ministar Shari’ar dai ta taba yin murabus sabaoda abin da ta kira banbancin ra’ayi tsakanina da gwamnatin Mwai Kibaki a wancan lokaci.

Shi kuwa Ruto, wato mataimakin shugaban Kenya na yanzu, ya nada attajiri Rigathi Gachagua a matsayin mai taya shi takara.

Ana dai kallon Gachagua a matsayin kwararre a fannin tattaro jama’a domin samun kuri’unsu tun daga tushe, kuma ya taba rike mukami a gwamnatin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.