Isa ga babban shafi

Raila Odinga zai kauracewa muhawara tsakaninsa da William Ruto

A Kenya ,daya daga cikin yan takara a zaben Shugabancin kasar Raila Odinga ya yi watsi da tayi da aka masa na halartar muhawarar da aka shirya tare da zargin abokin takarar sa William Ruto da shirin yin amfani da wannan dama don yi masa batanci tare da Ambato batutuwan da suka jibanci rashawa.

William Ruto daya daga cikin 'yan takara a zaben Kenya
William Ruto daya daga cikin 'yan takara a zaben Kenya © william Ruto twitter
Talla

An dai bayyana cewa  Raila Odinga da mataimakiyar sa za su gudanar da  Martha Karua za su gudanar da wani taron siyasa kan tsaye ta talabijen  daga wasu unguwanin birnin Nairobi  a mai makon muhawarar da abokin takarar ya yi watsi da ita.

A watan Mayu ne shekarar 2022 ne Manyan ‘yan takarar zaben shugaban kasa a Kenya sun zabi abokan tsayawa takararsu, inda Raila Odinga ya zabi wata fitacciyar mai gwagwarmayar kare hakkin mata, yayin da abokin adawarsa, William Ruto ya zabi wani kwararren masanin yakin neman zabe.

 A watan maris na shekarar bana ne shugaban kasar mai baring ado Uhuru Kenyatta ya bayyana goyan bayan sag a abokin adawar sa Raila  mai shekaru 77,sanarwar da kawo karshen  dangantaka tsakanin Shugaban kasar da mataimakin sa mai ci William Ruto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.