Isa ga babban shafi

Bam ya kashe mutane bakwai a arewacin Togo

Mahukunta a kasar Togo sun kaddamar da bincike a game da mutuwar yara 7 da kuma raunata wasu 2, bayan wata fashewar da aka samu a yankin arewacin kasar kusa da iyaka da Burkina Faso.

Wani sojan kasar Togo.
Wani sojan kasar Togo. AP - BEN CURTIS
Talla

Lamarin dai ya faru ne a cikin daren asabar zuwa wayewar garin ranar lahadi, lokacin da yaran ke kan hanyar komawa gida daga bikin da suka je a wani kauye mai suna Natigou da ke lardin Tone, wanda a cikin watan da ya gabata aka ruwaito cewa ‘yan ta’adda sun kai hari kan jami’an tsaron kasar.

Yaran dai shekarunsu sun kama  ne daga 10 zuwa 15, inda da farko aka bayyana cewa sun taka nakiya ce da aka binne a kan hanya, to sai dai daga bisani wasu bayanai sun ce ga alama yaran sun hadu da ajalinsu ne sakamakon harbi daga sama, harbin da ake cewa wani jirgi maras matuka ne ya jefa bam a kansu.

To sai dai har zuwa wannan lokaci babu tabbas ko bam da ake jefa daga sama ne ya yi sanadiyyar mutuwar wadannan yara, yayin da ma’aikatar tsaron kasar ta sanar da fara bincike a kai.

Hakazalika sanarwar ma’aikatar tsaron, ta gargadi jama’a da su guje yin tafiye-tafiye a cikin dare a wannan yanki da ke fama da ‘yan bindiga masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.