Isa ga babban shafi

Kungiya mai alaka da IS ta dau alhakin harin ta'addanci a Togo

Wata kungiyar ta’addanci da ke Mali, mai alaka da Al-Qaeda ta dau alhakin harin da aka kai kasar Togo a watan da ya gabata.

Dakarun Togo a wurin da aka kai harin ta'addanci a kasar.
Dakarun Togo a wurin da aka kai harin ta'addanci a kasar. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Kungiyar Jama'at Nasr al-Islam wal Muslimin tana ta fadada ayyukanta a cikin ‘yan kwanakin nan, inda take barazana ga arewacin kasashen Benin, Ivory Coast, Ghana da Togo.

Gwamnatin Togo ta tabbatar da harin ta’adancin da ya auku ranar 11 ga watan Mayu a garin Kpekankandi,  kusa da iyaka da Burkina Faso, inda ‘yan ta’adda ke da yawa.

Hukumomin Togo sun ce  dakarun Togo  8 ne suka mutu, 13 suka samu raunuka.

Wata majiya daga gwamnatin Togo ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa kimanin mahara 60 bisa babura ne suka kai wa dakarun Togo hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.