Isa ga babban shafi
Togo-Ta'addanci

Farmakin 'yan ta'adda ya kashe Sojin Togo 8 a iyakar Burkina Faso

Wasu ‘yan ta’adda da ake zargin magoya bayan kungiyar da ke da alaka da Alqa’ida ne, sun kai hari tare da kashe sojojin Togo 8, baya ga raunata wasu 13 a wani yanki da ke gab da iyakar kasar da Burkina Faso.

Wasu Sojin Togo.
Wasu Sojin Togo. AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Wannan ne dai karo na biyu a cikin watanni 6 da masu da’awar jihadin ke kai wa kasar ta Togo hari tare da kisan jami'an tsaro a wani yanayi da ba safai al'ummar kasar suka saba gani ba.

Rahotanni sun bayyana cewa dandazon ‘yan ta’addan rike da makamai ne suka farwa wani karamin sansanin soji da ke Kpendjal ne tare da kisan Sojin baya ga jikkata wasu da dama.

Masan ana alakanta farmakin da hannun wata karamar kungiya da ke biyayya ga al Qaeda a kasar M ali.

Duk da cewa makamantan farmakin ba sabon abu ba ne a yankin yammacin Afrika amma a kasar Togo ba safai aka saba ganin irinsa bad ai dai lokacin da hare-haren ta’addanci ke ci gaba da tsananta a kasashen yankin.

A wani taron hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afrika cikin makon jiya ministan tsaron Ghana Dominic Nitiwul y ace cikin shekaru 3 da suka gabata yankin ya gamu da makamantan hare-haren har sau dubu 5 da 300 wanda ya haddasa asarar rayukan mutane fiye da dubu 16.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.