Isa ga babban shafi
Togo

Gwamnatin Togo ta koma teburin sulhu da 'yan adawa

Wakilan gwamnatin kasar Togo da na 'yan adawa sun koma teburin tattaunawa domin sasanta rikicin siyasar kasar bayan tsaikon da aka samu na watanni uku.

Shugaban Togo Faure Gnassingbé.
Shugaban Togo Faure Gnassingbé. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Fadar shugaban kasar  ta sanar da komawa teburin tattaunawar bayan isar masu shiga tsakani wato shugaban kasar Ghana Nana Akkufo-Addo da takwaransa na Guinea Alpha Conde zuwa birnin Lome.

Sanarwar ta ce, bayan tattaunawa da bangarorin da ke rikicin, shugabannin za su gabatar da rahoto ga taron shugabannin Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma wadanda ke jagorancin kawo karshen rikicin.

Gwamnatin Togo ta sake jaddada matsayinta na kin amince wa da duk wani yunkuri wanda zai sa ta sauya kundin tsarin mulkin kasar, matakin da ake ganin zai zama babban tarnaki wajen kulla wata yarjejeniya.

'Yan adawa na bukatar ganin an koma amfani da kundin da ya tanadi wa’adin shugabancin kasa sau biyu kawai, amma shugaba Faure Gnassingbe da ke wa’adi na uku yaki amince wa da haka.

Tun bayan samun 'yancin kan Togo, iyalan Gnassingbe ne ke jagorancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.