Isa ga babban shafi
Togo

Tattaunawa domin sulhunta rikicin siyasar kasar Togo

A wannan laraba manzannin musamman na kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Yammacin Afirka Ecowas ko Cedeao za su isa birnin Lome na kasar Togo, domin farfado da tattaunawar sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan adawar kasar.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo (dama) da takwaransa na Guinee Conakry Alpha Condé (hagu)
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo (dama) da takwaransa na Guinee Conakry Alpha Condé (hagu) AFP/Philippe Wojazer/Daniel Leal-Olivas
Talla

Shugaban Ghana Nana akufo-Addo da takwaransa na Guinee Conakry Alpha Conde, za su yi kokarin sake ganawa da wakilan gwamnatin Faure Ngassingbe da kuma ‘yan adawa da ke fafutukar ganin an yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara kafin zabubuka masu zuwa.

A farkon wannan wata na yuni, wata tawagar Cedeoa karkashin jagorancin Jean-Claude Brou ta ziyarci kasar Togo inda ta gana da wakilan jam’iyyun adawar kasar 14, da kungiyoyin fararen hula da kuma bangaren gwamnati dangane da wannan batu.

Bayanai na nuni da cewa babban abin da ke kawo cikas ga wannan tattaunawa da aka fara tun cikin watan fabarairun da ya gabata shi ne ko za a bai wa shugaba Faure Gnassingbe damar sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2020 ko kuma a’a.

‘Yan adawa dai na ganin cewa dole ne shugaba Gnassingbe ya sauka daga mulki karshen wa’adinsa a shekara ta 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.