Isa ga babban shafi

IS ta dauki alhakin kashe majinyata 12 a gabashin Jamhuriyar Congo

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a garin Lume dake gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, cikin sakon da ta wallafa shafinta na Telegram, a ranar Asabar din da ta gabata.

Sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a garin Mwenda da mayakan ADF suka kaiwa farmaki a cikin watan Mayu.
Sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a garin Mwenda da mayakan ADF suka kaiwa farmaki a cikin watan Mayu. AFP via Getty Images - ALEXIS HUGUET
Talla

A ranar Juma'ar da ta gabata, wasu shaidu biyu suka tabbatar da cewa, maharan sun kashe akalla majiyyata goma sha biyu a wani asibiti cikin dare, inda suka dora alhakin harin kan mayakan ADF masu ikirarin kishin Islama da ke kawance da kungiyar IS.

Sai dai mai magana da yawun sojojin Jamhuriyar Congon ya ce maharan sun fito ne daga wata kungiyar mayakan sa-kai a gabashin kasar dake hada kai da ADF tare da amfani da salo iri daya.

Kakakin sojin Anthony Mualushay ya kara da cewa, sojojin sun kashe mayaka uku tare da kama daya yayin da suka mayar da martani kan harin da aka kai a garin Lume dake lardin Kivu ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.