Isa ga babban shafi

'Yan gudun hijiran Afirka za su fuskanci krancin abinci - MDD

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa 'yan gudun hijira a gabashi da yammacin Afirka ka iya fuskantar tsananin karancin abinci saboda karuwar karancin kudade.

Sansanin 'yan gudun hijira a Kamaru.
Sansanin 'yan gudun hijira a Kamaru. © AFP - Alexis Huguet
Talla

Kashi uku cikin hudu na 'yan gudun hijira a gabashin Afirka da shirin Majalisar Dinkin Duniya ke tallafa musu, an rage musu abinci da kashi 50 cikin 100, a cewar hukumar, inda wadanda ke Habasha, Kenya, Sudan ta Kudu da Uganda suka fi fuskantar matsalar.

Daraktan hukumar, David Beasley, ya ce a yankin yammacin Afirka, musamman Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Mali, Mauritania da Nijar hukumar ta rage yawan adadin agajin da take bayarwa.

Hakan ta sanya WFP ta nemi da a ba ta dala miliyan 426 domin dakile yunwa a Sudan ta Kudu, inda aka kwashe shekaru ana rikici da ambaliya ya tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu.

Ta ce sama da kashi biyu bisa uku na al'ummar kasar na bukatar agajin jin kai, inda ake sa ran mutane miliyan 8.3 da suka hada da 'yan gudun hijira za su fuskanci matsananciyar yunwa a bana.

MDD ta ce yakin da ake yi a Ukraine ya kara tabarbare matsalar 'yan gudun hijira a duniya da kuma hadarin yunwa, ba wai kawai samar da karin 'yan gudun hijira miliyan shida ba ne a yayin da fararen hula ke tserewa yankunan da ake rikici, amma wajen kara farashin kayayyaki musamman hatsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.