Isa ga babban shafi
Mali-Mauritania

Mauritania na neman bahasi kan kisan al'ummarta a Mali

Mauritania ta zargi Sojojin Mali da cin zarafin jama’arta bayan zanga-zangar da suka gudanar a birnin Bamako kan kisan sunkurin da suka zargi ma’aikatan kasar da aikatawa a kansu.

Mauritania na zargin Sojojin Mali da kisan jama'arta yayin zanga-zangar kasar.
Mauritania na zargin Sojojin Mali da kisan jama'arta yayin zanga-zangar kasar. AFP - EMMANUEL DAOU
Talla

Ma’aikatar wajen Mauritania da ke birnin Nouakchott ta yi sammacin jakadan Mali a kasar don ba ta bahasi kan yadda bayanai ke cewa ana samun bacewar tarin ‘yan Mauritania baya ga wasu da ake tsintar gawarwakinsu.

Dubban ‘yan Mauritania ne suka yi dandazo a gab da fadar shugaban kasa don kalubalantar abin da suka kira kisan mummuken da jami’an tsaron Mali ke musu a kwanakin baya-bayan nan.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar na rike da kwalaye dauke da rubutun kawo karshen yi musu kisan mummuke a kudancin birnin Adel Bagrou da ke gabashin Mali.

Wani dan Majalisar Mauritania ya ce zuwa yanzu ‘yan kasar 15 aka yiwa kisan gilla a Mali kari kan wasu mutum 7 da aka kashe a watan janairu.

Ko cikin watan Janairun da ya gabata sai da wani babban jami’in gwamnatin Mauritania ya yi tattaki zuwa Mali don tattaunawa da jami’an tsaron kasar kan yadda ‘yan kasar ke rasa rayukansu, sai dai duka da alwashin da mahukuntan Mali suka dauka na bayar da kariya, an ci gaba da samun mutuwar mutanen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.