Isa ga babban shafi
Mali

Mali ta ce sojojinta ba su yi kisan kiyashi a yankin tsakiyar kasar ba

Gwamnatin Mali ta musanta zargin da ake yi wa sojojinta na yi wa fararen hula da dama kisan gilla a yankin tsakiyar kasar a farkon watan Maris.

Sojojin Mali yayin atsaye a yankin Mopti dake tsakiyar Kamaru.
Sojojin Mali yayin atsaye a yankin Mopti dake tsakiyar Kamaru. AP - Francois Rihouay
Talla

Sanarwar ta biyo bayan matakin da rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yanke a ranar Juma'ar da ta gabata, na gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa mutane da dama a kauyukan da ake yankin Diabaly.

Wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta a wannan makon, ya nuna gawarwakin mutane da dama da aka kone su, bayan rufe musu idanu tare da daure hannayensu wuri guda. Wasu daga cikinsu kuma an ga ramuka a bayan kawunansu.

Wani jami'i a a yankin na tsakiyar kasar Mali, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an gano gawarwakin ne a daren ranar Talatar da ta gabata, kuma ana kyautata zaton sune wadanda sojojin Mali suka kama wasu a ranar 20 ga watan Fabrairu, wasu kuma a ranar 1 ga watan Maris.

Sai dai, gwamnati kasar ta yi fatali da zargin, tare da bayyana shi a matsayin karya tsagwaronta.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta sha zargin sojojin Mali da kashe fararen hula da kuma wadanda ake zargin mayakan sa kai ne a tsawon shekaru goma da suka shafe suna yaki da kungiyoyin da ke da alaka da Al Qaeda da kuma IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.