Isa ga babban shafi
Mali - tsaro

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da harin da ya kashe sojojin Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kazamin harin ta’addancin da ya hallaka sojin kasar Mali kusan 30 a Mondoro dake tsakiyar kasar.

Wani sojan Mali kan hanyar Gao da Kidal, Yulin 2013.
Wani sojan Mali kan hanyar Gao da Kidal, Yulin 2013. AFP PHOTO / KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Wakilin Sakatare Janar na Majalisar na musamman akan aikin zaman lafiyar dake gudana a Mali, ya gabatar da sakon ta’aziyar Majalisar ga gwamnatin rikon kwaryar Mali da kuma jama’ar kasar tare da iyalan sojin da suka rasa rayukan su.

Wakilin ya dada jaddada aniyar rundunar MINUSMA ta Majalisar wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin Mali.

Rundunar sojin Mali tace sojoji 27 suka mutu, yayin da wasu 33 suka samu raunuka sakamakon harin Yan ta’addan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.