Isa ga babban shafi

Umaro Sissoco Embalo ya tsallake rijiya da baya a Guinea Bissau

Shugaban kasar Guinea-Bissau ya ce ya tsallake rijiya da baya sakamakon yankurin juyin Mulki da yace an dau tsawon sa'o'i biyar ana luguden wuta wanda acewarsa lamarin ya yi sanadiyar kashe ko jikkata mutane da dama a kasar ta yammacin Afrika.

Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló yayin taron manema labarai
Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló yayin taron manema labarai © AFP/AFPTV/Aliu Embalo
Talla

An ga mutane suna arcewa daga yankin fadar gwamnatin, kasuwanni da bankuna  sun rufe kofofinsu, a yayin da motocin soji  cike da dakaru su na ta shawagi a unguwannin yankin.

Umaro Sissoco Embalo ya shaida wa manema labarai cewa, yunkuri ne na masu adawa da yakin da yake yi da cin hanci da rashawa da kuma fataucin miyagun kwayoyi.

Shugaban kasar Guinea Bissau  Umaro Sissoco Embalo
Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo SEYLLOU AFP

Shugaban yace, yanzu haka dai kura ta lafa kuma yana cikin koshin lafiya. Da suke mayar da martani a game da wannan lamari, kungiyar ECOWAS  da Tarayyar Afirka sun yi tir da yunkurin na soji, inda suka bukace su da su koma barikokinsu, suna mai kashedin cewa za su dora alhakin duk wani abin da ya sami shugaba Embalo a wuyarsu.

Babban birnin Bissau ranar daya ga watan Fabrairu 2022
Babban birnin Bissau ranar daya ga watan Fabrairu 2022 LUSA - ANTÓNIO AMARAL

Sakataren majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres, wanda ya bayyana damuwa a kan abin da ke faruwa a Guinea Bissau, ya yi kira da a girmama dimokaradiyya.

Kasar Guinea Bissau mai yawan mutane miliyan 2, wadda Portugal ta yiwa mulkin mallaka tana yamma da kasar Senegal,  kuma ta fuskanci juyin mulki har sau 4 tun bayan da ta samu yancin kai a shakarar 1974.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.