Isa ga babban shafi
Guinea Bissau

Jam'iyya mai mulkin Guinee Bissau ta ruga kotu

A jiya juma’a jam’iyya mai rijaye a Guinee Bissau ta ruga kotu inda ta shigar da kara dangane da zaben kasar da ya gudana.Jam’iyyar PAIGC dake da rijaye a majalisa ta bayyana cewa zaben Shugabancin kasar da ya gudana na tattare da kuskure.

Jam'iyya mai mulkin kasar Guinee Bissau
Jam'iyya mai mulkin kasar Guinee Bissau https://www.facebook.com/apupdgb.comunicacao
Talla

jam’iyya mai mulkin kasar a karkashin inuwar tsohon Firaminista kuma shugaban Majalisa Domingos Pereira ta bayyana cewa ta malaki sheidu dake tabbatar da cewa zaben ba a yi shi ba bisa gaskiya.

Sai dai hukumar zaben kasar ta ayyana dan takarar adawa tsohon Firaminista Umaro Sissoco Embalo a matsayin mutumen da ya lashe zaben zagaye na biyu a ranar 29 ga watan Disemba da ya gudana tareda lashe kusan kashi 53 da dingo 55 na kuri’u da aka kada. Sabon Shugaban kasar da za a rantsar da shi a watan Fabarairu ya cira yanzu haka zuwa kasashen Senegal,Congo da Nageria inda ake sa ran zai gana da Shugabanin wadanan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.