Isa ga babban shafi
Guinea Bissau-Portugal

Mutane 300,000 na fuskantar karancin abinci a Guinee Bissau - MDD

A kasar Guinee Biseau,sama da Mutane 300,000 ne yanzu haka ke bukatar agajin gaggawa kamar yadda Hukumar abinci ta Duniya ta sanar.Kasar Guinee Bisseau na daya daga cikin kasashen da hukumar majalisar ta bukaci a taimakawa da abinci, ganin cewa akwai mutanen da yawan su ya kai 300, 000 dake fuskantar karanci abinci. 

Matsalar karancin abinci a Jamhuriyar Nijar
Matsalar karancin abinci a Jamhuriyar Nijar www.unicef.org
Talla

A cewar kakaki hukumar abinci dake Birnin Geneva, har ya zuwa yanzu babu wata kasa ko kungiya da ta ce uffan kan batun taimakawa wadan nan mutanen da abinci.
Kamar yadda yake bayyane hukumar abinci ta duniya, wato World Food Programme ta shigar da kokon bara zuwa kasashen Duniya da kuma bukatar kudin da suka kai miliyan 7 na kudin Amurka.

Kasar Guine Bisseau dai na daya daga cikin kasashen da talaucin ya yiwa katutu a Duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.