Isa ga babban shafi
ECOWAS-Guinea Bissau

An yi musayar wuta a wani barikin sojan kasar Guinea Bisau

Rahotanni daga kasar Guinea-Bissau na nuna cewa wata musayar wuta da aka yi a wani barikin soji da ke kusa da wani filin saukar jiragen saman babban birnin kasar, ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida.Da misalin karfe hudun safiyar yau, wasu ‘Yan bindiga da ba san ko suwaye ba, suka kai harin kan barikin, inda suka kwashe kusan sa’a guda suna musayar wuta da sojoji, kana daga baya maharan suka tsere,Rahotanni sun tabbatar cewa an kashe mutune biyar daga cikin maharan, a yayin da daya daga cikin masu gadin barikin sojin ya rasa ransa.Mutane da dama na ganin, harin bai rasa nasaba da wani Karin girma da aka yi a rundunar sojin kasar, wanda bai ma wasu daga cikin sojojin dadi ba.A dai watan Aprilun daya gabata ne, sojoji suka yi juyin mulki a kasar ta Guinea - Bissau. 

Sojojin kasar Guinea-Bissau
Sojojin kasar Guinea-Bissau Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.