Isa ga babban shafi

Fira Ministan Guinea Bissau da ministocinsa sun kamu da coronavirus

Gwamnatin Guinea Bissau tace Fira ministan kasar Nuno Gomes Nabiam tare da wasu ministocinsa guda 3 sun kamu da cutar coronavirus.

Fira Ministan Guinea Bissau Nuno Gomes Nabiam.
Fira Ministan Guinea Bissau Nuno Gomes Nabiam. REUTERS/Joe Penney
Talla

Ministan lafiyar kasar Antonio Deuna yace ministan cikin gida Botche Cande na cikin ministoci 3 da wannan annoba ta rutsa da su, kuma yanzu haka an killace su a wani Otal dake Bissau.

Ana kyautata zaton shugabannin sun kamu da cutar ce sakamakon mu’amalar da suka yi da wani babban jami’in ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar, wanda tuni yam utu.

A baya bayan nan kasar Guinea Bissau ta sanar da samun mutane sama da 73 da suka kamu da cutar coronavirus, yayinda guda daga cikin su ya mutu.

Masana sun sanya Guinea Bissau cikin jerin kasashen Afrika dake kan gaba wajen fuskantar hadarin barkewar rikicin shugabanci, la’akari da cewar sau 16 ana yunkurin kifar da gwamnati, wanda 4 suka yi nasara, tun bayan samun ‘yancin kan kasar daga a shekarar 1974.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.