Coronavirus ta kusan kama 'yan Afrika miliyan 10-WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi hasashen cewa, za a iya samun karuwar mutane milyan 10 sabbin kamuwa da cutar coronavirus a nahiyar Afrika nan da watanni 3 zuwa 6 masu zuwa duk da kasasncewar nahiyar mafi karancin masu dauke da cutar a yanzu.
Wallafawa ranar:
Hasashen WHO na zuwa ne duk da matakan da gwamnatocin kasashen nahiyar ke dauka na killace jama'a a gida don dakile yaduwar cutar.
Sai dai Michael Yao, shugaban Sashen Agajin Gaggawa na WHO, reshen Afrika ya ce, ba lallai hasashen hukumar ya iya zama gaskiya ba, kamar dai hasashen da ta yi lokacin annobar Ebola na yiwuwar mutuwar miliyoyin jama'a amma kuma hakan bai tabbata ba, saboda matakan kariyar da jama'a suka dauka.
Acewar Michael Yao, matakan lafiyar da ake dauka da ma damarar da jama'a suka daura na hana yaduwar cutar matukar suka ci gaba da tabbata ko shakka babu, hasashen hukumar ba zai tabbata ba.
Kawo yanzu dai fiye da mutum dubu 17 aka tabbatar sun kamu da cutar ta corona a nahiyar Afrika ciki har da 900 da suka mutu, adadin da ke nuna nahiyar a matsayin mafi karancin masu dauke da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu