Jacob Zuma na ci gaba da samun kulawa daga likitoci
An yiwa tsohon Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma tiyata a yau asabar kasa da mako daya da baro gidan yari inda ake tsare da shi. Tsohon Shugaban mai shekaru 79 zai fuskanci wasu jerrin ayyuka daga likitoci da za su sake duba lafiyar sa nan gaba kamar dai yada majiha daga gidan yarin da ake tsare da shi ta sanar.
Wallafawa ranar:
Jacob Zuma na fuskantar dauri na watanni 15 biyo bayan kin bayyana gaban alkali dangane da tuhumar da ake yi masa na sama da fadi tareda karbar na goro kama daga shekara ta 2009 zuwa 2018.
Tun ranar 8 ga watan yuli aka garzaya da shi gidan yari Estcourt dake gabashin kasar ta Afrika ta kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu