Gwamnatin Sudan za ta mika Omar al-Bashir ga kotun duniya
Gwamnatin Sudan ta ce za ta mika tsohon shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir ga kotun duniya da ke Hague don ya fuskancin shari’a dangane da zarge-zargen aikata laifukan yaki da na cin zarafin bil’adama.
Wallafawa ranar:
Ministar harkokin wajen kasar ta Sudan Mariam al-Mahdi ce ta tabbatar da hakan ga babban mai shigar da kara na kotun Karim Khan da ke gudanar da ziyarar aiki a birnin Khartoum.
Mariam ta ce baya ga al-Bashir akwai wasu mutane biyu wato Ahmed Haroun tsohon gwamnan Kordafan ta Kudu da kuma tsohon ministan tsaro Abdl Rahim Mohamed Hussein.
Kotun duniya ta ICC dai ta shafe shekaru akalla goma tana neman tsohon shugaba al-Bashir mai shekaru 77 a duniya ruwa a jallo bisa zarginsa da kisan kare dangi, laifukan yaki da cin zarafin bil adama a yankin Darfur.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane dubu 300 aka kashe yayin da wasu miliyan 2 da dubu 500 suka rasa muhallansu a rikicin Darfur, wanda ya barke a yankin yammacin kasar cikin 2003.
Sojoji sun kifar da gwamnatin al-Bashir tare da tsare shi a watan Afrilun 2019 bayan watanni hudu ana zanga-zangar gama gari a duk fadin Sudan don adawa da mulkinsa.
Tun a shekarar 2009 kotun ta ICC ta bayar da sammacin kamo al-Bashir saboda laifukan yaki a Darfur, daga baya ta kara da kisan kare dangi a kan tuhumar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu