Isa ga babban shafi
Sudan

Omar al Bashir zai gurfana a gaban Kotu

Babban mai shigar da kara a Sudan Alwaleed Sayed Ahmed Mahmoud ya ce akwai yiwuwar cikin mako mai zuwa su gurfanar da hambararren shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir gaban kotu don amsa tuhume-tuhumen da ake masa ciki har da taimakawa ayyukan ta’addanci baya ga kisan kare dangi.

Hambararren shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir
Hambararren shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

A cewar Alwaleed Sayed yayin jawabinsa gaban manema labarai a birnin Khartoum bayan kammala ganawa da shugabancin mulkin soji na kasar, baya ga al-Bashir akwai manyan jami’an gwamnati akalla 41 da za su fara fuskantar shari’a kan laifuka masu alaka da cin hanci da rashawa.

Kalaman na Alwaleed na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin sojin ta Sudan ta dakatar da shirinta na tabbatar da wata doka da za ta bayar da damar karbe wasu muhimman gurare daga hannun sojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya da ke aiki a Afrika ciki har da shalkwatar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.