Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu - Bore

'Yan sanda sun yi arrangama da masu kokarin wawashe rumbun barasa

'Yan sanda a garin Durban na Afirka ta Kudu sun harba harsasan roba, da hayaki mai sa hawaye, don hana wani gungun mutane satar abin da ya rage a wani rumbun adana barasa.

‘Yan sanda tsaye kan wadanda ake zargi da wawure dukiya a wata cibiyar kasuwanci da ke garin Alexandra, a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu. 12 ga Yuli, 2021.
‘Yan sanda tsaye kan wadanda ake zargi da wawure dukiya a wata cibiyar kasuwanci da ke garin Alexandra, a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu. 12 ga Yuli, 2021. AP - Yeshiel Panchia
Talla

Da farko dai an wawure shagon ne cikin makon da aka yi mummunan tashin hankali a yankin KwaZulu-Natal na Afirka ta Kudu wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 200.

Rahotanni daga Afrika ta Kudu sun ce an samu lafawar boren magoya bayan tsohon shugaba Jacob Zuma dake neman sakinsa daga gidan Yari kan tuhumar sabawa umarnin kotu na kin mika kansa bisa zargin cin hanci da rashawa.

Sai dai wasu daga cikin mazauna yankunan da aka samu tashe tashen hankula na yin amfani da damarsu wajen afkawa manyan shagunan kayayyaki da sauran rumbuna domin wawashe ababen da aka adana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.