Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Wasu miyagu na neman yamutsa Afrika ta Kudu - Ramaphosa

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce wasu mutane ne suka kitsa tashe-tashen hankulan da suka yi sanadin mutuwar mutane fiye da 212 a kasar a cikin mako guda.

Cyril Ramaphosa yayin magana da ‘yan jarida a ziyarar ranar Juma’a da ya kai cibiyar kasuwanci dake Durban da masu bore suka wawashe.
Cyril Ramaphosa yayin magana da ‘yan jarida a ziyarar ranar Juma’a da ya kai cibiyar kasuwanci dake Durban da masu bore suka wawashe. © REUTERS
Talla

Ramaphosa yayi zargin ne a lokacin ziyarar da ya kai lardin KwaZulu-Natal domin ganewa idanunsa irin barnar da wasu magoya bayan tsohon shugaba Jacob Zuma suka tafka.

Cyril Ramaphosa ya ce abubuwan da suka faru biyo bayan daure tsohon shugaban Afirka ta Kudun shiryasu aka yi inda ya kara da cewar tuni hukumomi suka gano wasu dake cikin gungun da suka tayar da fitinar da ta lakume rayukan mutane sama da 200 a kasar.

A halin da ake ciki Jami’an tsaron Afirka ta Kudu sun kame mutane sama da 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.